Umar M Shareef, fitaccen mawakin Hausa ne, na soyayya ko kuma na nanaye, sannan an sanshi a matsayin dan wasan kwaikwayo na masana’antar kanywood. Umar M Shreef yana da kyakkyawar alaka da dukkan yan wasan kwaikwayon Hausa na kanywood wanda ya samu lambar yabo daga bangare daban-daban.
Tarihi
An haifi jarumin a shekara ta 1989 a karamar hukumar Igabi ta jahar kaduna, shahararren mawakin Hausa ne sannan kuma jarumi ne a masana’antar kannywood wanda ya shahara a kasar Najeriya da sauran kasashen afrika. Jarumin kuma mawaki yana da mabiya a kasashe da dama a fadin duniya, Wanda a kullum burinsa bai wuce ya ga ya burgesu ba.
Karatu
Jarumin ya fara karatun Qur’ani tun yana karami a gida kafin ya shiga makarantar boko wacce izuwa yanzu ya kai matakin digiri wanda ya ke yi a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU)
Wakoki
Asalin fara wakarsa ta dalilin wata yarinya da yake so amma ya kasa sanar mata har izuwa lokacin da ya yanke shawarar tinkararta amma sai bata fito ba hakan ya sa ya tafi yana rera waka. Jarumin ya jima yana Waka amma tauraronsa ya fara haskawa ne a shekara ta 2007 sannan yayi wakoki da dama a bangare daban-daban na soyayya, siyasa, da wakokin biki da suka haɗa da;
- Jinin jikina
- Sareena
- Jirginso
- Ruwan dare
- Hafiz
- Ciwon idanuna
- Arewa
- Ciwon so
- Mariya
- Wazana ba kaina
Albums/Kundi
Sannan yanzu yayi albums da dama kamar su:
- Farin Jini 2022
- Wakokin Umar M Shareef Guda 10 Na Shekarar 2020
Sunan Kundi/Album | Shekarar fita |
---|---|
Bako | 2018 |
Tsintuwa | 2016 |
Masoya | 2016 |
Kalaman bakina | 2017 |
Ni Da Ke | 2018 |
Babbar Yarinya | 2017 |
Kuyi Hakuri | 2017 |
Haɗaka
Sannan yayi wakoki da mawaka da dama kamarsu;
- Nura M Inuwa
- Lilin Baba
- Abdul D one
- Hamisu Breaker
- Adam A Zango. Da sauransu
Fina-finai
Ya fito a finafinai da dama kamarsu;
- Mansoor
- Sareena
- Mujadala
- Hafeez
- Mariya
- Tsakaninmu
- Ciwon idanu na
- Kar ki manta Da ni
- Nass
Bugu da kari mafi yawan fina-finansa ya fito ne a companin FKD wanda mallakin Ali Nuhu ne. Sannan shi ne mamallakin Shareef studio wanda sun shirya fina-finai kamar su
- Zarah
- Jinin jikina
Karramawa
Jarumin ya sha karban kyautar karramawa da kyautar girmamawa da dama a fadin duniya daga kungiyoyi da dama kamar su
-kannywood films award
-afrikan actors
Da sauransu
Iyali
Umar M Shareef yana da mata daya Maryam da yara biyu jarumin da kuma Hafsat.
Ya kasance daga cikin manyan jaruman da suka ziyarci sassa daban-daban na duniya. Jarumin ya ziyarci kasashe da dama wadda suka hada da :
Niger, Ghana, Cameron, Chad, da sauransu.