Rayuwar Farko
An haifi Breaker a shekarar 1992 a Dorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Najeriya.
Karatu
Ya halarci makarantar firamare da sakandare a Dorayi duk da har zuwa yau mawakin babu wani rahoto da yake nuni da ya cigaba da karatun jami’a.
Fara waƙarsa
Breaker ya fara Waƙa ne tun lokacin yana makarantar sakandare kuma ya yi waƙoƙi da dama kafin ya fara fitar da album Kuma waƙar sa da ta yi tashe sama da ko wacce ita ce Jaruma musamman a cikin Hausawa. A wannan shekara ta 2020, Jaruma ita ce waƙar Hausa ta soyayya da aka fi kallo da sauraro domin saida takai wani mataki a YouTube da babu wata waƙar da ta taɓa kaiwa a ƙanƙanin lokaci a tarihin waƙoƙin hausa.